Sharfadi Technology Nigeria
→Home
Assalamu Alaiku Barka da zuwa wannan bangare Inda zaka samu bayanai Akan Abubuwan da suka shafi Facebook da dukkan dabaru da ake amfani da su a shafin InshaAllahu,
**YADDA ZAKA BUDE FACE BOOK**
Mataki na 1:-

Da farko zaka ziyarci www.facebook.com
→Shiga nan don zuwa kai tsaye

kana zuwa zaka ga an rubuta:-

Facebook

Create Account

Get Facebook Mobile and browse faster.

Email address or phone number

Password

Log in

New to Facebook?

Create New Account

Forgotten Password?
Help Centre
English (UK)· Français (France)· Português (Brasil)· More…
Facebook ©2015

Se ka shiga Create new Account ko Create Accont zaka ga an rubuta haka;-

Facebook
Sign up for Facebook

First Name:

Surname:

Email Address or Phone Number:

Gender:
Date of Birth:
dd/
mm/
yyyy

New Password:

By clicking Sign Up, you agree to our Facebook Termsand that you have read our Privacy Policy, including our Cookie Use. You may receive SMS Notifications from Facebook and can opt out at any time.

Sign Up

Already have an account?

Se ka cike wajen suna na farko idan kana son Amfani da suna 3 to ka sanya sunaye guda 2 wajen suna na 2 kuma se ka sanya suna na uku:

misali:

wajen suna na 1: Basheer Journalist
wajen suna na 2: Sharfadi

se su ha du su bada,

Basheer Journalist Sharfadi

sannan wajen

Email or phone number

Idan kanada email se ka sanya email din idan baka dashi ka sanya lambar wayarka,

Sannan wajen Gender se ka za6a kai mace ne ko na miji male/female

Date of birth se ka sanya ranar Haihuwarka da watan da kuma shekarar kamar yadda suka baka guraben da xaka saka ajere,

Password se ka sanya password dinka wanda kasan baxaka manta ba sannan shawara kada ya gaxa kaiwa Abu 8 a password din sannan ka tabbata ka riqe abinda ka rubuta a password din,

Dagana se kayo qasa xakaga an sanya 'Sign Up' se ka shiga,
,

Bayan ka shiga za kaga sun rubuta maka:-

'Confirm Phone Number

Let us know this phone number belongs to you. Enter the code in the text sent to' se su sakaambar taka ko E-mail din a nan (Nigeria).

Wrong number?

Enter confirmation code

Confirm

Send Code Again

Confirm by Email

Change Phone Number

Search

Help

Settings & Privacy

Back to Etisalat Homepage
Report a Problem
Terms & Policies
Logout (Sunan da ka saka a nan)

Back To Top

To kana ganin wannan bayanin to sun tura maka da saqo ta wayarka / Email din ka Idan Email ne agun xaka ga sunan Emal dinka yayi kala se ka hau kai xe kai ka kawai se kayi Comfirm,

Idan Lamba ce to se ka sauko ka koma Inbox msg din ka ka kofi lambaobin da suka turo maka guda 5 In kuma Bwayarka tana Minimizing se kayi kaje ka dauko 'Code' din in kaxo se ka sanya a gurbin da suka baka bayan ka saka se kai comfirm,

KARIN BAYANI:

Na san wani idan ya sauka to ba ze iya dawowa kan gurin da ze sanya 'Code' din ba to ga yadda zaka yi,

Idan ka sauko ka dauki Lambobin se ka koma kan oper/browser se ka shiga History zaka ga guri na qarshe da ka sauka seka danna Insha Allah ze mai da kai gurin,

Bayan Kayi Comfirm zakaga sun turo maka akwatin rubutu sunce kayi search na Freind se ka saka sunan wanda ka ke so kayi Addin misali:-

'Lawal Mamman Bilbis'

kana sanyawa zaka ga sun turo maka shi se kayi Adding bayan kayi kuma se su turo maka da Abokai da yawa ka za6a, Amman kada kayi Adding na Mutane da yawa a lokacin saboda yawan yin Adding na mutane yana sanyawa a rufe maka Account din ka,

Sannan za su iya turo maka ka cike sunan gari makaranta Aiki dasauran su sannan kuma za su nuna maka guri inda zaka koma Kan wayarka ka dauko hoton da zaka dora a 'Propile Picture', In kaga dama kuma duk wannan cika-ciken ba se kayi ba kana duba qasa zaka ga 'Skip' se kayi ta yi har ka wuce daga nan zaka ga ta nuna maka Haka:-

Facebook Search
Home Edit Profile Find Friends Messages Notifications Chat
Add 9 More Friends (6/15)

Then you'll see their updates in News Feed.

Find Friends

Search for Friends

SearchTip: Enter a friend's name

People You May Know

Awaisu Al'arabee Fagge
Jibwis Nigeria
Add Friend

Lawal Mamman Bilbis
Jibwis Kano
Add Friend

Basheer Journalist Sharfadi
Jibwis Social Media Kano
Add Friend

See All Suggestions

Share with: Friends
Post

Add Photos
Check In
More

Basheer Journalist Sharfadi
GASKIYA ZAKZAKY BAYA TSORON ALLAH,
.
.
Biyo ni kasha labari,........Continue Reading,

To Idan kaga sun baka makamantan Irin wadannan bayanan to shi kenan ya gama buduwa sauran ka nutsuwa ka gudanar da shi,


**HANYA TA BIYU DA ZAKA BUDE FACEBOOK HANYA MAFI SAUQI**
Hanya ta 2 kuma mafi sauqi wajen bude face book Itace:-

Ka bude facebook ta Application din sa Idan ka fahimci bayanin yadda ake bude wa na farko da muka kawo baka buqatar wani bayani Sai dai a gaya maka yadda zaka samu Application din to idan kaje Www.facebook.com zaka ga sun rubuta maka:-

'Install Facebook on your sunan wayarka and browse faster kawai se kai down loading ko kaje babban shafin mu www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com domin yin downloading kai tsaye,

Bayan kayi download kana bude shi zaka ga ya baka zabi,

Login or Sign Up,

Se ka shiga sign Up InshaAllah zaka ga sauqin sa matuqar ka fahimci bayanin baya,

Don qarin bayani da kuma sada zumunta da mu kayi can qasa kayi register da mu don cigaba da samun bayanai In kayi register ka jira za'a yi maka approve,

YADDA ZA KAYI RUBUTU KAYI POSTING DIN SA A FACE BOOK
Kamar yadda muakayi bayani a sama bayan ka kammala bude facebook ga Abubuwan da zaka gani D.s to Akwai buqatar kasan Inda za kayi rubutu To Daman kada ka manta Idan z yi Login wato kana son hawa facebook dinka to zaka je www.FB.com ko www.facebook.com duk Abu daya ne Idan Accont dinka yana kai zaka ga ya kaika kai tsaye idan kuma ba ya kai ko kayi log out To ze baka gurbi guda biyu wajen:-

Email or Phone Number

Password

Wajen Email se ka sanya Numbarka Idan Email ne kuma se ka sanya E-mail din qasa kuma ka sanya Pasword,

Bayan ka sa zakaga an rubuta:

'LoGin' a kasa se ka shiga InshaAllah zaka ga ya kaika irin gun da mukayi bayani a sama wato Facebook Home,

In kaje nan se ka kula sosai zaka ga Irin wannan Akwatin a qasa ko kuma a sama zakaga an saka 'Propile' shima In ka shiga zaka ganta,




Post
Se ka shiga a kwatin ka tsara rubutun ka kai dai kawai ka nutsu gurin babban baqi kada kayi qaramin baqi ka tsarashi sosai kuma ka dinga bada space Sannan ka tabbata kayi me ma'ana wanda jama'a zxasu amfana,

Idan ka gama kawai se ka hau kan 'Post' Din da aka rubuta akusa da akwatin shikenan kayi poast a wall ko nace propile dinka,

YADDA ZAKA BADA SPACE DA SAKIN LAYI A RUBUTUNKA
X2 1black 1X2 2white
X2 karamaAnd kypd
Na san da yawa daga cikin Y'an uwa muna amfani da daya daga cikin wadannan 'Key pad' To ga Irina masu amfani da qaramin keypad In kana rubutu zaka danna 'space' se ka danna '0' sau 2 zaka ga ta bada space Idan kuma zaka bada sakin layi se ka danna '0' sau 3 wata kuma sa 4, Amman wannan Shut cut ne,

Yadda zaka bada sakin layi shine ka shiga Symbol kamar zaka sa ka Alam kamar su:

':;?!%=_ da sau ran su a ciki zaka ga kibiya irin wanna:-

Sakin layi
Kana sanya wannan kibiyar zaka ga ta baka sakin layi a rubutun naka,

Ga masu Amfani da waya me babban Keypad A6an garen hannun dama saman control kuma zaku ga wannan kibiyar sannan kuma ga 'Space' nan za kuga madannin da yafi ko wanne girma na layin qarshe wanda yake a tsakiya shi zaku danna ya baku space,

Ga masu Amfani da wayoyi qirar 'Android' kuma a hannun daman za kuga wannan kibiya wadda kuke yin 'sending' da ita a watsap, sannan kuma ga space nan a qasa kamar irin na wadda muka kawo a baya,

YADDA ZAKA DORA HOTO KAYI POSTING DASHI
Idan ka hau facebook dinka wajen inda akwatin rubutu take kamar yadda muka kawota da kuma inda zaka ganta a face book,

A kasan akwatin zaka ga an rubuta 'Add photos' se ka shiga za kaga irin wannan akwatin ta dauko hoto a kasanta kuma da akwatin rubutu kamar haka:-








Post
YADDA ZAKAYI DOWNLOADING DIN HOTO A FACE BOOKIdan ka shiga kan Hoton da kake son yin DownLoading zaka ga an rubuta 'View Full Size' se ka shiga zaka ga ,

Open ko Save,

Se ka za6i wanda zaka yi a ciki in ya gama shikenan ya dawo kan wayar ka,

Ga masu Amfani da Uc Browser kawai In ka hau kan Hoton ka danna Lamvba daya '1' zaka ga save as..... Se kayi shike nan,

YADDA ZAKA MAIDA RUBUTUNKA KOWA ZE IYA GANI BA SE IYA FREIND DINKA BA
Idan ka duba saman akwatin rubut zaka ga an rubuta:-

'Share with: Freind And Freind'

se ka hau kan Freind And Freind zaka ga ya baka za6i kamar haka:-

Public
Freind And Freind
D.S

se ka hau kan 'Public' shike nan duk abinda kayi ze tafi ga kowa da kowa, Shikenan,

YADDA ZAKA KULLE FREIND DINKA BABU WANDA ZE GAN SU SAI KAI KADAI
Idan ka shiga propile dinka se ka shiga 'Freind' zaka ga an rubuta haka:-

Who can see your friend list? Freind Of Freind

se ka shiga Freind of Freind zaka ga an baka uption:-

Freind of freind
Public
Only me

se ka sanya only me shikenan ko nawane freins dinka ba ze gani ba se dai yaga wadanda shima freind din sa ne,

NA BUDE FACEBOOK DA E-MAIL KO NUMBER AMMAN E-MAIL DIN KO LAMBAR TA 6ATA INA TSORON AYI MI BLOCKING DIN ACCOUNT DIN SHIN YAYA ZANYI??
Idan ka bude da email ne to ka shiga wannan jan rubutun kawai se ka sanya wani email din sannan ka sanya password din ka se kayi saving shikenan,
→Shiga nan

Idan kuma da lambar waya ne kuma layin ya 6ata to se ka shiga wannan jan rubutun na qasa se ka sanya wata lambar sannan ka sanya pass word dinka se kayi save,
→Shiga nan

FREIND DINA SUN CIKA KUMA MUTANE DA YAWA SUNA SO SU DINGA GANIN RUBUTU NA SHIN YAYA ZANYI??
Kawai ka shiga wanna jan rubutun na kasa se ka sanya 'FOLLOW' wadda ita wata dama ce da zata bawa mutane damar yin Following dinka inda za su dinga ganin dukkan abinda kayi,

→Shiga nan

YADDA ZAKA CANJA SUNANKA NA FACEBOOK
Kawai shiga wannan jan rubutun na kasa se ka saka sunan da kake so sannan ka sanya password dinka se kayi save,
→Shiga nan

YADDA ZAKA CANJA PASSWORD DIN KA NA FACEBOOK
Ka shiga wannan jan rubutun na kasa se ka sanya tsohon Password din ka sannan ka sanya sabon da kake so se kayi save,
→Shiga nan

NA MANTA PASSWORD DINA NA FACE BOOK SHIN YAYA ZAN YI??
Idan ka je www.facebook.com kamar zakayi 'Login' a kasa zaka ga an rubuta:-

Forgot Password?

Se ka shiga za ka ga an rubu to maka ka sanya lambar ka ko E-mail dinka se ka sanya wanda ka bude da shi,

A kasa zaka ga an rubuta coninue se kayi. To za su turo maka da 'Code' akan Numbar ko Email din se kaje ka dauko kamar dai na bude facebook,

Bayan ka dauko se ka saka 'Code' din sannan kayi Comfirm to za su baka gurare ka rubuta sabon Password din sannan ka mai-mai ta shi a kasa misali:-

New Password

Repeat New Password

Comfirm New Password

Guri na farko da na biyu se ka sanya Sabon Password din da kake so guri na uku kuma shi zaka shiga shi kenan ka gama, shiga wannan jan rubutun donmin canjawa,
→Shiga nan

AN RUFE MIN FACEBOOK DINA SHIN YAYA ZANYI??
Da farko dai ya kamata kasan cewa yana daga abinda yake sawa a rufe ma facebook Account din ka,

Yawan yin Adding din mutane (SendingFreind Request)

Yawan yin Join Group sosai D.s

Wa dannan abubuwa ka kula dasu sosai ka dinga yin su a hankalce,

Sannan Facebook Idan suka rufe ma ka Accont kai tsaye kaje

www.facebook.com

Kayi login za su gaya maka abinda ya samu account din naka Wani sukan yi 'Susspending' din Account din da na tsawon wani lokaci ta yadda ba zasu bude maka shi ba har sai lokacin yayi ,

Sannan zasu iya maka tambayoyi akan bayanan ka ko abokanka na facebook ko hotunan su ko su nemi ID Card dinka D.s

Sannan yana da kyau ka iya amsa security Chek wanda shima sunayi kuma shi yafi yawa kuma shine yake ko ina a Internet za'a iya yi maka shi don haka ma zamuyi bayanin sa a nan,

Idan kaga sun rubuta ma ka daya daga cikin wadannan:

Enter text on image:

(Enter this into the box below)

Type this text

'aWaISu'

Idan ka rubuta AWAISU KO awaisu to ka wadi is wrong se dai ka rubuta irin wannan:-


Ma'ana dole irin wanda suka baka shi zaka yi musu guri karamin baqi ka saka qaramin baqi haka gurin babban baqi shima,
INA SO NA BUDE GROUP A FACEBOOK ANJE HAR CAFE AMMAN ABIN YA CI TURA SHIN YAYA ZANYI??
Idan ka hau Facebook dinka a sama zakaga an rubuta Group Amman Idan kaima kanada abokai da yawa Amman idan kai ma Irina ne to kana hawa facebook din se kayi can qasa zaka ga an rubuta haka misali ni:-

Abu Hafsah Al'kanawi Profile· Photos
Friends
Groups
Events
Pages
Pokes
SMS
Notes

to se ka shiga cikin Group zaka ga An rubuta 'Create Group' kana shiga zaka cike sunan group da public ko close ko secret Dasauransu in ka gama ka danna Create shike nan, se kayi Adding din members ka sanya Description, sannan kaje kayi search zaka ga group din,

Shiga nan domin budewa kai tsaye

→Shiga nan

YADDA ZAKA BUDE SHAFI (Page) A FACEBOOK
Idan ka hau Facebook dinka a sama zakaga an rubuta Page Amman Idan kaima kanada abokai da yawa Amman idan kai ma Irina ne to kana hawa facebook din se kayi can qasa zaka ga an rubuta haka misali ni:-

Abu Hafsah Al'kanawi Profile· Photos
Friends
Groups
Events
Pages
Pokes
SMS
Notes

to se ka shiga cikin Page zaka ga An rubuta 'Create Page' kana shiga zaka cike sunan Page da Categoreis Dasauransu in ka gama ka danna Create shike nan, se kayi Invite na Freind din ka In kana so sannan ka sanya Description, sannan kaje kayi search zaka ga Page din,

Sanna Page ko abu daya ka cike ya budu indai kayi search zaka ganshi,

Shiga nan somin budewa kai tsaye,

→Shiga nan

YADDA ZAKA SAKA ADMIN A GROUP DA PAGE
GROUP
Da farko in ka shiga Group din ka se kayi can kasa zaka ga an rubuta:-

Group Menu
Info
Admin Panel
Add Member
Members
Photos
Events
Files

To se ka shiga members kana shiga zaka ga sunayen members daman kada ka manta se ka fara Adding din mutum a group sanna zakayi masa Admin ma'ana dole se mutum yana cikin group misali:-

Sani Abu Unaisa
Admin · Added by basheer journalist sharfadiabout 2 months ago
Remove· Make as Admin

Awaisu Al'arabee Fagge
Added by Basheer Journalist Sharfadi about 3 months ago
Remove· Make Admin

Lawal Mamman Bilbis
Joinedabout 3 months ago
Remove· Make Admin

Umar Lajin Kofar wambai
Added by Abu Hafsah Alkanwiabout 3 months ago
Remove· Make Admin

Sunusi Sa'idu Sheka
Added by Awaisu Faggeabout 3 months ago
Remove· Make Admin

Tasi'u Aliyu Bebeji
Added by Lawal Bilbisabout 4 months ago
Remove· Make Admin

See More


To se ka duba sunan wanda zaka yiwa Admin baka ganshi ba kayi see more saboda yana tafiya ne da Alphabetic,

In kaga sunan wanda zaka yiwa se ka hau kan 'Make as Admin' se kai Comfirm din sa shike nan InshaAllah,

Kar kamanta kayi register da mu domin samun qarin baya nai

PAGE
Idan ka hau kan shafin ka misali sunan shafin ka:

'IZALA IKON ALLAH'

To kana hawa zaka ga an rubuta haka:-

Page
Activity 20
IZALA IKON ALLAH
Religion
Post
Photo
Edit Page
More
What's on your mind?
Post
Add Photos
More
About· Photos
Religion
More Information
3,718
likes
Lawal Mamman Bilbis , Haphsah Vaava Eedrys and 498 others like this.
Promote Your Page
Photos by IZALAH IKON ALLAH
80
36 posts to Page recently
Hafizu Idris Sani and 35 others
Recent Posts by Others

IZALA IKON ALLAH
Posted by Basheer Journalist SharfadiSunday at 16:42·
**MEYE LAIFINA ??? Kashi na 2**
.
.
DAGE WANDO SHINE SUNNAH SHI YASA MU YAN IZALA MUKA RIKE SAU DA KAFA,
.... Continue Reading'


Idan kaga makamancin wannan to se ka shiga ''More'' din nan na sama na kusa da 'edit page' kana shiga zaka ga an rubuta,


More
Liked
Share
Edit Settings
Create New Page
Add to Favourites

Se ka Shiga 'Edit settings' kana shiga zaka ga an rubuta:-

Settings
General
Page Info
Notifications
Page Roles

Se ka shiga 'page roles' wato na karshe kana shiga shima zaka ga an rubuta misali kamar haka:-

Page Roles

Add Person to Page
Current People

Lawal Mamman Bilbis
Admin
Edit

Umar Lajin Kofar Wambai
Admin
Edit

Jibwis Kano Municipal
Admin
Edit


In kai kadai ne Admin to kai kadai zaka gani a ciki bayan ka shigo nan to zaka ga an rubuta misali kamar haka:-

Add Page Admin

Select Friend
Search

Suggested Friends· All friends

Abba A Yakub
Set as Admin

Ahmad Ali Aliyu
Set as Admin

Awaisu Al'arabee Fagge
Set as Admin

Kana ganin wannan kawai se ka shiga 'set as Admin' da yake kasan sunan wanda kake so kasa ka Admin din, In baya nan se kai search dinsa matuqar yana cikin Freind dinka zaka gan shi bayan kayi haka zaka ga sun rubu ta maka haka:-

Enter Password
For your security,
please re-enter your password to continue.

Continue
Forgotten Password?

Seka saka Facebook Password din ka kana sawa za kaga sun baka za6i kamar haka misali na dauki sunan Awaisu:-

Add Person to Page

Awaisu Al'arabee Fagge

Page Roles
Admin
Editor
Moderator
Advertiser
Analyst

Add

se ka za6a a cikin wadannan muqaman se ka za6a Admin ko Editor? Amman in baka san mutum ba to ka bashi editor shine yake da dama yayi posting Amman bashi da dama ya qwace ma ka page din ka,

YADDA ZAKA YI COPY DIN RUBUTU
Hanyoyin Yin Copy din rubutu sun kasu akalla guda Uku Amman zamuyi magana akan guda biyu saboda sune suke kowa ma ze iya yi.

Ya dan uwa zanso ka qudurce niyyarka ta taimako da daukaka Addinin Allah wannan copy Hanya ce da zaka tallata ka watsa da'awar sunnah Lungu da saqo kana cikin gida,

Da Farko akwai Copy Ta Opera:-

Anayin sa da opera daga kan

Opera mina 4, 5, 6, 7, 8, D.s

Sannan opera ta Android ko Black Berry suma suna yi Idan baka da ita shiga wannan Hoton na Opera dake Kasa Domin Yin Downloadin din ta,


YADDA ZAKA YI AMFANI DA ITA BAYAN KA YI DOWNLOADING
Bayan kayi downloadin din ta za kayi login kamar yadda ka saba a facebook din ka (ba wai ina nufin se an hau facebook ake copy ba),

Idan ka hau kan Rubutun da zaka yi copy se ka danne madannin tsakiya 'OK' in kuma 'Touching' ce wayar ka danne farkon rubutun ko kasan she har se kaga ya kawo wata kibiya ya rubuta maka,

Select and Copy ko start Copy ko Copy,

kana ganin Haka kawai se ka fara copa zaka ga Inda kake kofa yayi Kala. In ka kai qarshen Inda kake son kayi copy zaka ga ta rubuta:-

'Use ko copy'

In Use ne kana shiga zxaka ga Copy se kayi Idan copy ne kawai se kayi copy shi ke nan,

YADDA ZAKA LIQA RUBUTUN DA KAYI COPY (past/kayi posting din sa)


Send
Bayan kayi copy din rubutun ka se kaje inda kake son yin posting din sa misali Wall dinka ko Group ko page ko inbox da sauran su idan dai ka shiga dukkan gurin da ake yin rubutu misali akwatin nan ta sama to in ka hau kai kamar zakai rubutu wata zaka danna' option' a nan zaka ga an saka'past' se ka danna zaka ga rubutun ka ya dawo kwai se ka tura in post ne in msg'ne se kayi shi kenan,

Wata kuma kawai in ka hau kan akwatin rubutu se ka danne tsakiya 'OK' kamar yadda kayi da zakayi kopy zakaga ta nuna maka 'Past' se ka shiga shi kenan zaka ga rubutun ya dawo,

HANYAR COPY TA BIYU KUMA MAFI SAUQi
Wannan kuma copy ne wadda ake yin sa da 'Uc Browser' wadda zaka iya yin copy din Abu ma sama da daya akan ta da farko dai akwai buqatar ka yI downloadin dinta domin yin downloading shiga wannan hoton nata na kasa,


Bayan kayi Downloading se ka bude ta kayi login a facebook dinka tunda muna magana ne a kan face book,

Idan ka ha kan inda zaka fara copy din rubutun kawai se ka danna Lamba '1' za kaga sun maka rubutu kamar haka:-

Open in New
Close Tab
Save link As
Search
Select and copy
Share.

To se ka shiga Select an copy zaka ga ab rubuta:-

Select Text
Copy Link

Se ka Shiga Select Text xaka ga wata kibiya ta kawo se ka saita kibiyar inda kake son fara copy din se ka danna 'OK' Start kenan se kai copy In ka gama zaka dannan Hannun hagu madannin saman kira zaka ga 'CopyK' se kayi shi ke nan.

Bayan kayi Copy ita na kamar wancan In ka je gurin rubutu se dai ita ba se ka danne ba in kaje akwatuin rubutu kawai ka danna Lamba '1' zaka ga:_

Accounts
Copy
Past
Edit
Clipbord

Se ka shiga 'Past' zaka ga rubutun ya dawo Idan kuma Kayi rubutun ne a cikin Akwatin se ka danna lamba '1' Kana son kayi Copy se ka shiga 'Copy' shi kenan yayi maka copy Idan gyarashi zakayi se ka shiga 'Edit' Shi kuma Account da kuka gani Idan za kuyi Login din kamar Face book kayi Log Out in zaka dawo indai ka taba login da Uc din kawai ka shiga Account zaka ga Email din ka ko lambar ka kawai pasword zaka sa ba se ka rubuta wancan ba,

Se dai Ita 'UC' ga masu Original Waya tana iya ajiye muku rubutu ko da kun sauka kun dawo yana nan amman in ka dau ki rubutu sannan kana kan Uc din baka sauko ba wayarka ta mutu to rubutun ya tafi amman in ka sauka bayan kayi copy to rubutun naka yananan har sai in kai kaga damar goge shi,

Sannan Masu babban Kepad Akwai Shut cut wajen copy kawai ku danna Harafin 'C' ze kaiku kai tsaye kawai Start zakuyi,

YADDA ZAKA YI POSTING A GROUP DA YAWA
Tunda ka iya Copy to da mana ka riga kayi copy din Rubutun ka to kawai duk Group/Page din daka shiga se kayi 'Past' kayi posting shi kenan kayo back ka kara shiga wani shima haka,

Amman ko akwai yadda ake posting a Group da yawa kuma a lokaci Daya??

YADDA ZAKA YI COPY DIN LINK
Shi 'Link' ko kuma nace 'Ma6allin Liqau' Kamar yadda ake kiran sa a hausa, Wata Hanya ce ko kuma nace mahada Saboda duk wani shafi da za mu hau yanada Adress din sa shine link wanda in kanada wannan link din kai tsaye ze kaika gurin, misali:-

http://basheerjournalistsharfadi.xtgem.com

Wannan Link ne kuma anayin copy din sa misali in kaga wani abu a internet ko face book da muke magana kuma baka so ya 6ace maka kawai se ka dau link din sa, kana zuwa kuma zaka saka shine a wajen Adress na www.,

Ga masu Opera In kahau shafi ka danna Hannun Hagu zaka ga wani rubutu a sama :- Http://facebook..... To kana hawa kansa ka danna 'Option' zakaga ya saka ma ka 'Copy' se kayi to shikenan daman wannan ne 'Link' din, To duk Inda kaje kayi posting dinsa duk wanda ya shiga can gurin ze maida shi,

Ga masu Uc Browser kuma idan kazo kamar zakai 'Copy' zaka ga 'Copy Link' se kayi shikenan Idan kuma Babban Keypad ne da kai ka Danna Harafin 'P' za ka ga link din sannan zaka ga copy a karshensa se ka hau kan copy din shike nan,

Shima Ana yin 'Past' din sa kamar yadda ake na Rubutu:,

Sannan Link yana iya karyewa musamman in kaimasa copy irin na rubutu amman in kaga ya bada space to se ka goge space din in ba haka ba baxe bude ba se ka dauka kaje kayi edit ka goge duk inda ya bada space,

YADDA ZAKA YI TALLAN SHAFIN KA A FACE BOOK DA YADDA ZAKA RUBUTA SUNAN MUTUM DA KOREN RUBUTU
Shima Hanyoyi da zaka Tallata shafi suna da dama Amman zamu dauki guda daya wanda ake yayi yanzu,
Misali Idan ka hau shafin ka ka dauko Link din shafin ka kamar haka:-

https://m.facebook.com/profile.php?id=656168224503950

A ciki kaga wadan su Lambobi to Sune Id din Page din se ka dauki lam bobin Da farko se ka sanya wadannan A lamomin:-

@[ se ka saka lambobin Anan bayan ka gama saka lambo bin se ka sa :0 se ka rufe Braket din ka ] t o ze baka sunan shafin, A Face book Misali:-

@[656168224503950:0]

Se Ya bamu Haka:-

Jibwis Social Media Kano Municipal Nigeria

Shi kenan Shi kuma Na mutum Kawai ka hau kan propile din wanda kake son dauka ka hau kan hoton sa ko wanne in dai shi yayi Upload se ka dauko Link din kamar Haka:-

https://m.facebook.com/photo.php?fbid=1418963528338406&id=100006743161487&set=a.1376016465966446.1073741827.100006743161487&refid=17

Kaga wadan su Lambobi Kamar Wadan can to shi Ba na Farkon zaka dauka ba na biyu wadanda suka fara da 10000 kenan zamu dauki wadannan :-

100006743161487

Suma zaka yi musu kamar wancan na page sannan page irin sa ake yiwa group Kenan zamuyi kamar Haka misali:-

@[100006743161487:0]

Se ya bamu:-

Basheer Journalist Sharfadi

Shi kenan Idan ka Iya Wannan to se kai Hada su kayi copy ka tsara yadda zakayi Taan se ka sa wannan Yadda mutum kawai shiga ze yi,

Za mu kawo sauran A gaba,


YADDA ZAKA YI UPLODING DIN AUDIO A FACEBOOK

FACEBOOK MAGIC
Wadannan 'Code' zamu kawo wanda dayawa daga ciki suna Amfanine kawai ga masu yin Facebook ta Opera da dangogin ta banda masu yi ta Application sannan Ta opera zaka iya Comment ko Msg ko Posting duk ze bada ma'ana a ciki,

Sanna duk Abinda muka kawo zamu fadi Yadda yake kawai kwafa zakayi In kai posting zaka ga MA'ANAR da zai bayar,

Idan kasa wannan:-

@[2015:0]

A face book To ze gaya maka sunan wannan shekarar A yaren FaceBook Misali:@-

[2015:0]

In kai post din sa zakaga abinda ze bayar,

Shi kuma wannan In kai post din sa

[[f9Heart]]

ze fitar maka da Alamar 'LOVE' babba me kayu sosai,

Shi kuma wannan

[[f9Like]]

In kai Post din sa ze fitar maka da Alamar Hannu, Me kala Kuma babba mai kyau,

Shi kuma wannan

<3

ze fitar Maka da Alamar 'Love' Amman karami,

Shi kuma wannan

@@[1:[0:1:Basheer]]

In kana so rubutu ba Link ba yayi kore o seka saka shi wajen da aka saka basheer se ka cire ka sanya Rubutun ka ze baka koren rubutu,

Shi kuma wannan

[[f9.Num1]]

In ka cire Lamba dayan nan ka sanya lambar da kake so ze baka hoton lambar Yayi mata Kala kuma me kyau ya qawata ta,

Shi Kuma wannan

<(")

Ze baka Hoton Yar Karamar Aku,

Shi kuma Wannan

(y)

ze baka Hoton Hannu Dan Karami, Like,

Shi kuma wannan

@[0:0:]

In kana so kayi Comment ba tare da ka rubuta komai ba wato 'Empty Comment' se ka saka shi to kawai sunan ka za'a gani,


Shi kuma wannan

[[264528750353172]]

In ka Saka shi ze baka 'Good Night' Da rubutu me kala Kuma Me kyau,

Shi kuma wannan

[[168836883325952]]

Ze baka Irin KOREN point din nan Da yake nuna mutum yana Online,

Shi kuma wanna

[[518743568233542]]

Ze baka zanen Kibiyoyi masu kyau da kala,

Shi kuma

[[1405973432952403]]

Ze baka Rubutun 'Assalamu Alaikum' me kala kuma me kayu sosai,

Shi kuma wannan

[[1424392074439152]]

Ze baka Alamar Tambaya me kyau sosai,

Zamu cigaba InshaAllah domin Cigaba da samun bayanai kayi Register da mu,

DUNIYAR WATSAP
YADDA ZAKA BUDE WATSAP

Idan baka da Watsap shiga wannan Hoton na sama kayi Downloading Amman ka sani ba ko wacce wayace take watsap ba,

Idan kayi downloading kana bude shi zaka ga ya nuna maka wajen saka number a sama kuma zaka ga 'Contry code', se ka shiga ka canja ka saka 'Nigeria' in kuma Nigeria yake, Shikenan seka saka numbarka misali Lambarka Itace:-

08173559393
+1248173559393

TO SE KAYI irin wannacan na biyun wato ka cire '0' na farko, kenan ka maida ita haka:-

8173559393,

Daga nan se ka danna 'OK' shikenan ze nuna maka optin ko kira ko msg inkira kake so se ka za6a ko sms,

In sun kiraka zasu gaya maka Numbobi. Se ka saka su shikenan ze yi update in yagama se ka saka suna da hoto shikenan,

YADDA ZAKA BUDE GROUP A WATSAP
Idan ka hau WastAp din ka se ka danna 'option' ko kuma nace 'menu' madanni na hannun hagu zakaga 'Create Group' se ka shiga Kawai sunan group din zaka cike se ka saka 'Icon' ma'ana Hoton da zakasa a propile din Group din shike nan,
YADDA ZAKA SANYA ADMIN SAMA DA DAYA A WATSAP
Bayan ka bude group a WatsAp kuma kanason ka qara wani a matsayin Admin Abinda za kayi kawai shine:-

Ka shiga Group Info ka hau kan members din Group din In ka hau kan sunan wanda kake son yiwa Admin din se ka danna 'Option' zaka ga :-

Remove
Make as Admin

se kai make as Admin kayi 'ok' shike nan,

Amman wannan yana tsayuwa ne kawai akan iya sabon WastAp wato wanda akai Update Idan naka be yiba to kayi Update dinsa,

YADDA ZAKA AIKA DA MSG GA DAUKACIN CONTACTS DINKA NA WATSAP A LOKACI DAYA
Bayan ka Hau WastAp din ka se ka danna 'Option' zaka ga:

Broad Cast List, ko
Create Broad Cast List, Ko
New Broadst List,

Duk wanda ka gani se ka shiga za ka ga gurin da zaka sa Suna se ka sanya sunan da kake so. Sannan kayi Adding din CONTACT din ka.

In ka gama kayi 'ok' to Duk sanda ka tashi tura saqo ko kayi Forward kawai se kai saerch Din sunan da kasa a Broad Cast din se kayi Sending shike nan duk xe je musu a lokaci daya,

Idan ka samu sabon Contact kana so ka saka shi a ciki kana shiga Broad Cast List din zaka iya karawa ko ka cire,


KAYI REGISTER DAMU DON CIGABA DA SAMUN BAYANAI


→Koma Saman Shafi
*Yi Register da mu*
* This is private forum. You have to be approved by administrator to view it.
Bloggers Chat Group
Please log in or sign up to chat

→Menu
→Home Page
→Duniyar Face Book
→Yadda zaka bude E-mail
→Wayar Hannu
→Internet Cheat
→Yadda zaka bude word press website
→Yadda zaka bude wapblog website
→Yadda zaka bude Xtgem website
→Website Code
→Website Colour Code
ISLAMIC DATE
phpimg2.php?it=rect&ic=
phpimg2.php?it&ic=yellow
| Manufofinmu |Tuntube mu |→Zaka iya bina ta Facebook


XtGem Forum catalog